Mutum 5 sun rasa rayukansu, wasu 10 sun samu raunika a hatsarin babban titin Legas zuwa Ibadan

Mutum 5 sun rasa rayukansu, wasu 10 sun samu raunika a hatsarin babban titin Legas zuwa Ibadan

- Mutane 5 suka kone kurmus a hatsarin da ya auku a babban titin Legas zuwa Ibadan

- Hatsarin ya faru ne da mota fara mai kirar Mazda wacce ta taho daga Sokoto

- Hatsarin ya auku ne sakamakon mugun gudu da kuma kubcewar motar daga matukin

Mutane 5 me suka kone kurmus inda wasu goman suka samu raunika a hatsarin da ya auku kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar juma'a.

Clement Oladele, kwamandan jami'an kiyaye hadurra na yankin ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai aukuwar lamarin a Abeokuta.

Oladele ya ce hatsarin ya auku ne wajen karfe 8:49 na safe kuma mugun gudu ne yayi sanadi.

Kwamandan ya ce ya shafi fasinjoji 18 ne, maza 17 sai mace 1.

Shugaban FRSC ya ce 10 daga cikin fasinjojin maza sun samu raunika inda biyar daga ciki, 4 maza sai daya mace suka ce ga garinku.

KU KARANTA: 'Yan majalisar wakilai sun nuna fushinsu ga shuwagabannin tsaron kasar nan

"Motar ta taho ne tun daga Sokoto inda ta tsaya ta diba fasinjoji a Ibadan."

"Motar fara kirar Mazda mai lamba WWD 302 na tunkarar Legas ne kafin ta kwacewa direban a Onigaari saboda mugun gudu. Ta ci karo ne da marabar titi inda ta wuntsila," in ji shi.

Oladele ya ce an kai wadanda suka samu raunin asibin koyarwa na jami'ar Olabisi Onabanjo inda aka mika gawarwakin ga ma'adanar gawarwaki na asibitin.

Shugaban ya ja hankali masu ababen hawa da su dinga tuki da lura ganin cewa har yanzu gyaran titin ake.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel