Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

Yadda yarjejeniya da aka kulla tsakanin tsohon gwamnan PDP da Buhari kafin zabe ta samu tangarda

- An gano cewa an kulla wata yarjejeniya tsakanin wani gwamnan PDP da wasu na kusa da Shugaba Buhari gabanin zaben 2019

- Yarjejeniyar dai itace samun goyon bayan tsohon gwamnan yayin da shi kuma za a nada shi gwamnan CBN

- Sai dai daga bisani bayan jam'iyyar APC tayi nasara a jihar tsohon gwamnan na PDP, ba a nada shi gwamnan na CBN ba

Wani tsohon gwamnan jam'iyyar PDP a daya daga cikin jihohin arewa yana cizon yatsarsa bayan wata yarjejeniya da ya kula da wasu na kusa da Shugaba Muhammadu Buhari gabanin zaben shugaban kasa na 2019 ta ruguje.

A yunkurin su na tabbatar da cewa Buhari ya yi nasara a zaben, mukarraban shugaban kasar sun tuntubi wannan tsohon gwamnan PDP inda suka nemi ya goyi bayan tarzarcen Buhari inda shi kuma suka masa alkawarin cewa za a nada shi gwamnan babban bankin kasa CBN.

The Nation ta ruwaito cewa tsohon gwamnan ya amince da alkawarin ya su kayi masa duba da cewa wa'addin gwamnan CBN, Godwin Emefiele na farko ta kusa karewa. Yana kuma ganin cewa ya cancani rike wannan matsayin.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci

Wasu 'yan jam'iyyarsa ta PDP sun zargi cewa yana kula wata alaka da jam'iyyar APC wato fadar shugaban kasa amma a lokacin ya tabbatar musu cewa ba bu wani abu mai kama da hakan da ke faruwa.

Da zabe ya zo, jam'iyyar APC tayi nasara a jiharsa. Jam'iyyarsa ta PDP kuma ta sha kaye hakan yasa wasu jiga-jigan jam'iyyarsa suka zargi shi da cin amanar jam'iyyar. A halin yanzu an juya masa baya a jam'iyyar PDP kuma wadanda suka masa alkawarin nadin mukami a gwamnatin APC sunyi watsi da shi duba da cewa an sake sabunta wa'addin Emefiele.

Yanzu an ce tsohon gwamnan na PDP ya zama saniyan ware a jam'iyyarsa kuma yana cikin bakin ciki domin akwai alamar an ci moriyar ganga ne an yar da korenta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel