An dakatar da tashin wani jirgin sama saboda wasu musulmi 2 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a Amurka

An dakatar da tashin wani jirgin sama saboda wasu musulmi 2 da ake zargin ‘yan ta’adda ne a Amurka

Wasu musulmi biyu mazauna garin Dallas a kasar Amurka sun hadu da wani abinda ya yi matukar bata masu rai a wani filin sauka da tashin jiragen sama.

Labarin da muka samu game da wannan lamarin shi ne an dakatar da jirgin nasu daga tashi, inda suke kokarin zuwa filin saukar jiragen birnin Dallas daga Birmingham saboda hankalin sauran fasinjojin bai natsu da su musulmin ba.

KU KARANTA:Duk mai fadin Buhari bai iya mulki ba makaryaci ne – Osinbajo ya yiwa Gumi martani

A lokacin da suka sauka daga jirgin jim kadan bayan an dakatar da tafiyar, jami’an tsaro ne ke biye da su duk inda suka shiga har ma wasu jami’an FBI suka tsaida su domin yi masu tambayoyi.

Abderraoof Alkhawaldeh, daya daga cikin masu magana da yawun musulmin garin Irving tare da Issam Abdallah, jagoran musulmin garin Dallas sunyi Allah wadan wannan abu da ya faru.

Sun kuma rubuta takarda zuwa ga ma’aikatar sufurin Amurka domin ganawa da ita a kan abinda ake yiwa mutanensu.

“Wannan abu shi ne abu mafi cin zarafi da wulakanci da na taba gani a rayuwata,” a cewar Abdallah da yake magana da wata kungiyar cigaban Dallas ranar Alhamis.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka ta ce kamfanin Mesa Airlines ne yake da alhakin jiragen da suka aikata wannan abu.

LaKesha Brown, mai magana da yawun gwamnatin kasar Amurka ta ce: “An dakatar da tashin jirgin ne a dalilin tsorata da wasu fasinjoji da matuka jirgin suka yi.”

Brown ta kara da cewa, babu wani abu da zai sa jirgi ya dag matukar akwai fargaba daga mutum daya cikin jirgin saboda babban burin kasar Amurka shi ne tsare rayukan ‘yan kasarta.

https://www.dallasnews.com/business/airlines/2019/09/19/two-muslim-men-say-american-airlines-canceled-their-flight-to-dfw-because-crew-didn-t-feel-comfortable-flying-with-them/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel