Akwai yiwuwar Najeriya ba za tayi bikin cika shekaru 100 da samun 'yanci ba - Bisi Akande

Akwai yiwuwar Najeriya ba za tayi bikin cika shekaru 100 da samun 'yanci ba - Bisi Akande

Tsohon mukadashin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Bisi Akande ya ce dukkan 'yan Najeriya suna rayuwa cikin fargaba ne inda ya yi gargadin cewa idan aka cigaba a haka Najeriya tana iya yin bikin cika shekaru 60 da samun 'yanci amma ba dole tayi na cika shekaru 100 ba.

A jawabin da ya yi a Lagos wurin kaddamar da wani littafi mai lakabin “The Bisi Akande Phenomenon?” ya ce shekaru 50 da suka shude na 'yan Najeriya suka rasu cikin jin dadi.

Tsohon gwamnan na jihar Osun ya ce lokaci ya yi da Najeriya za tayi bita ga garambawul kan dokokin kasar domin duk burbushin dokokin kama karya na mulkin soja ne.

Ya ce yana goyon bayan wadanda ke neman a yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul da ce cewa yin hakan a Najeriya ba abu bane mai sauki.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci a Delta

"Ya zama dole ayi bitan wasu abubuwa uku a kasar nan, na farkon su shine ilimi. Ilimin namu kawai ya kare ne daga koyon karatu da rubutu amma babu koyar hikima," inji shi.

Ya ce dole a mayar da hankali kan kimiyya.

Ya cigaba da cewa, "na biyu dokokin mu duk tsaffin dokokin sojoji ne kuma ba za a iya amfani da su a karkashin demokradiyya ba. Muddin bamu canja su ba demokradiyyar mu ba za ta inganta ba.

"Na uku shine batun addini, saboda yawancin addinan mu daga kasashen waje muka koyo su. Muna zaune cikin fargaba kuma idan akwai matsaloli a maimakon mu shiga dakunan bincike sai mu tafi coci da masalatai muna addu'o'i.

"Kasar da ke tafiya a haka za ta iya bikin cika shekaru 60 amma ba za ta taba yin bikin cika shekaru 100 ba. Ina ganin ya kamata a duba wadannan matsalolin; Ina goyon bayan yin garambawul na siyasa da kabilun mu amma suna da wahalan yi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel