Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar

Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar

- Hoton sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana a mataki na biyar a jerin hotunan manyan sarkunan jihar

- A ranar Alhamis ne aka sake sanya hotunan sarakan a dakin nadin sarautar jihar tun bayan da mabiya Ganduje suka cire hoton sarkin

- Sanya hotunan ne a jerin nan ya dawo da idanun mutanen gari

Hoton sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana a mataki na biyar a jerin hotunan manyan sarakunan jihar, jaridar Daily Nigerian ce ta lura da hakan.

Jaridar ta ruwaito cewa hoton Sanusi da aka saka a dakin nadin sarauta yayin nadin sarautarsa a matsayin Sarkin Kano da tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Kwankwaso a shekarar 2014.

Hoton yana dakin nadin sarautar ne har zuwa 2015 lokacin da Gwamnan jihar na yanzu, Abdullahi Ganduje ya hau karagarsa. An kuma jerasu ne da hoton gwamnan da na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar
Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar
Asali: Facebook

Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar
Ganduje ya kai Sarki Sanusi matakin karshe a jerin Sarakunan jihar
Asali: Facebook

KU KARANTA: 'Yan majalisar wakilai sun nuna fushinsu ga shuwagabannin tsaron kasar nan

Amma kuma, bayan Dan hargitsin da ya wanzu tsakanin Sanusi da Ganduje, magoya bayan Ganduje sun cire hoton Sarkin bayan da aka sanar da cewa Ganduje ne ya lashe zaben ranar 23 ga watan Maris.

Jaridar ta lura cewa, bayan karin manyan sarakuna 4 da gwamnatin jihar ta yi, gwamnatin jihar Kano din ta maida hoton Sanusi tare da sauran sarakunan a ciki da wajen dakin nadin sarautar a ranar Alhamis.

An kara da lura da cewa, hoton Sanusi, wanda shi ne jagoran sarakunan gargajiyan, ya bayyana a matakin karshe a jerin hotunan. Hakan kuwa ya jawo idanun mutanen gari.

Tsarin jerin hotunan na nuna, Aminu Ado Bayero; sarkin Bichi wanda shi ne a farko, Tafida Abubakar Autan-Bawo; sarkin Rano, sai Ibrahim Abdulkadir; Sarkin Gaya, biye da shi akwai Ibrahim Abubakar II; Sarkin Karaye sai na karshe Muhammadu Sanusi II; Sarkin Kano.

Idan zamu tuna, a ranar 8 ga watan Mayu, Ganduje ya kirkiro da masarautu 4 masu manyan sarakuna a jihar, wanda ake zargin yunkuri ne na ragewa Sarki Sanusi iko.

An samu sabani ne tsakanin shuwagabannin biyu a yayin yakin neman zaben gwamnan jihar, inda Ganduje ya zargi Sanusi da goyon bayan babban mai kalubalantarsa, Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel