Duk mai fadin Buhari bai iya mulki ba makaryaci ne – Osinbajo ya yiwa Gumi martani

Duk mai fadin Buhari bai iya mulki ba makaryaci ne – Osinbajo ya yiwa Gumi martani

Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Yemi Osinbajo a ranar Juma’a 20 ga watan Satumba, 2019 ya karyata masu ihun cewa Buhari bai san yadda ake mulki ba.

Ya kuma yi watsi da maganar cewa mukarraban wannan gwamnatin ta Buhari kansu kawai suka sani, inda ya ce gwamnatin tana gudanar da ayyukanta ne saboda cigaban ‘yan Najeriya baki daya.

Osinbajo ya kara da fadin, ayyukan da gwamnatin nan ke yi ya kamata a ce sun wuce matakin da suke a yanzu in banda wadansu masu hana ruwa gudu dake kawowa gwamnati cikas.

KU KARANTA:Assha! Bacin rai ya sa wani magidanci kashe surukarsa da kanwar matarsa da jaririn ta

Mataimakin shugaban kasan yayi wannan maganar ne a wurin bikin bizne Moroluke Fakoyede, mahaifiyar Sakataren hukumar EFCC wato Ola Olukoyede.

Osinbajo ya ce: “Buhari ya gaji mataccen tattalin arziki ne daga wurin gwamnatin da ta shude ta Goodluck Jonathan. Wannan dalilin ne ya sanya wasu abubuwa da Shugaba Buhari ya so yi bai samu damar aiwatar da su ba.

“Abinda wani na ji wani malamin addini ya fadi ya matukar bani tsoro tare da mamaki, inda yake cewa wai mu kadai ke jin dadinmu saboda muna bisa mulki. Sam wannan ba gaskiya bane, muna iya bakin kokarinmu domin ganin Najeriya ta cigaba.

“Bamu da wani buri da wuce cigaban ‘yan Najeriya. Dukkanin shirye-shirye rage fatara kamarsu TraderMoni da N-POWER mun fito da su ne saboda ‘yan kasa sun amfana. Haka kuma ba a nan zamu tsaya ba akwai wasu ire-irensu dake tafe.” Inji Mataimakin shugaban kasan.

A karshe Osinbajo ya kwantar da hankali ‘yan Najeriya ta hanyar ba su tabbacin cewa ko wannensu zai amfana da wannan gwamnati ta Shugaba Muhammadu Buhari.

https://punchng.com/its-not-true-that-buhari-doesnt-know-how-to-govern-osinbajo/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel