Gwamnonin APC sun shirya daukar salon mulki iri daya

Gwamnonin APC sun shirya daukar salon mulki iri daya

- Gwamnonim da aka zaba karkashin jam'iyyar APC sun rantsar da sabon kwamiti

- Kwamitin gwamnonin zai tabbatar da sun dau salon mulki iri daya a jihohinsu

- Gwamnonin sun tabbatar da zasu maida hankali a bangarorin kudin shiga, tsaro, ilimi da kiwon lafiya

Gwamnonin da aka zaba karkashin jam'iyyar APC sun rantsar da sabon kwamitin tabbatar da kafuwar aiyukansu iri daya.

Shugaban gwamnonin APC, Atiku Bagudu, ya rantsar da kwamitin a ranar juma'a a Abuja.

Kwamitin ya samu taimakon shugabancin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.

A jawabinsa, Lalong ya ce za a fifita fannonin kudin shiga, tsaro, ilimi da lafiya.

KU KARANTA: 'Yan majalisar wakilai sun nuna fushinsu ga shuwagabannin tsaron kasar nan

Ya ce, "Karbar kalubalen cimma manufar jam'iyyarmu ta APC, na zama jam'iyyar damokaradiyya mafi inganci, dole ne muka fito da tsare-tsaren cimma wannan manufa a matakin jiha. Tabbatar da cewa duk salon mulkinmu ya zama iri daya a duk jihohi shi ne jigon cimma manufarmu,"

"Tsakanin 2015 da 2019, a matsayinmu na gwamnonin cigaba, yakamata mu dau salo iri daya amma kuma abinda zamu fi dubawa shi ne kalubalen da jihohinmu ke fuskanta. Zaurenmu tuni ya aminta da wasu bangarori da zamu baiwa fifiko,"

"Bangarorin sun hada da karuwar kudin shiga, matsalar tsaro, ilimi da kiwon lafiya. Yakamata mu tabbatar da cewa bangarorin nan sun samu cigaba ba kadan ba cikin shekarun mulkinmu."

Yayin rantsar da kwamitin, Bagudu ya ce gwamnonin APC zasu tabbatar da cewa an samu cigaba mai yawa a jihohinsu duk da halin matsin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel