Adanan Menderes: Mutumin da yayi ma Musulunci hidima yar ya rasa ransa a sanadiyyar haka

Adanan Menderes: Mutumin da yayi ma Musulunci hidima yar ya rasa ransa a sanadiyyar haka

Masu iya magana na cewa kunne ya girmi kaka, a yau Legit.ng ta kawo muku labarin tsohon shugaban kasar Turkiyya, Adnan Menderes wanda ya jagoranci kasar daga shekarar 1950 zuwa 1960, kuma a cikin shekarun ya kawo sauye sauye masu ma’ana ga addinin Musulunci.

Shi dai Adanan ya kasance shugaba mai ra’ayin Musulunci, amma yayi zamani ne a lokacin da ake tashen Boko akida kamar yadda tsohon shugaban kasar Turkiyya Kemal Attaturk ya cusa wannan akida a tsakanin shuwagabannin kasar.

KU KARANTA: Ke duniya! Budurwa ta yi garkuwa da kaninta, ta nemi a biya naira miliyan 6 a Adamawa

Adanan Menderes: Mutumin da yayi ma Musulunci hidima yar ya rasa ransa a sanadiyyar haka
Adanan Menderes: Mutumin da yayi ma Musulunci hidima yar ya rasa ransa a sanadiyyar haka
Asali: Facebook

Daga cikin manyan ayyukan da Adnan yayi shine warware duk wasu tsare tsare da gwamnatocin Boko akida na su Kamal ta yi kamar su haramta kiran sallah da harshen larabci, rufe masallatai matsa ma masu addinin da sauransu.

Tarihi ya nuna a shekaru 10 da Adnan ya yi mulki, ya bude dubunnan masallatai da aka rufesu a baya don kuntata ma Musulmai, haka zalika ya tabbatar da mayar da kiran sallah cikin harshen larabci kuma ya sanya hakan a cikin kundin dokar kasar.

Ire iren ayyukan kwarai da yake yi yasa ya zamto barazana ga shuwagabannin kasar yan boko akida, inda aka samu wasu Sojoji 37 suka kifar da gwamnatinsa a ranar 27 ga watan Mayu 1960, inda suka kamashi tare da manyan jagororin jam’iyyarsa suka gurfanar dasu gaban kotun Soji, suka kuma yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 17 ga watan Satumbar yana dan shekara 61.

Sai dai kafin mutuwarsa, Adnan ya yi wani magana, inda yace: “Mutanen Turkiyya musulmai ne, kuma zasu cigaba da kasancewa musulmai har abada, don haka dole ne a tabbatar da kidar musulunci tare da koyar dasu ta yadda za’a janyo jama’anmu na yanzu da masu tasowa zuwa ga addinin Allah.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel