Ban san dalilin da yasa nake kashe mutane ba, inji fitinannen mai kisan kai

Ban san dalilin da yasa nake kashe mutane ba, inji fitinannen mai kisan kai

Gracious David West, babban dan ta'adda da aka kama a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, sannan yan sanda suka gurfanar dashi a ranar Juma’a yace an tursasa shi kashe yan mata ne a dakunan hotel domin daukar fansar mahaifiyarsa wacce yace ta mutu daga wani cuta bayan wasu mutane da ba a sani ba sun bata guba.

Da yake zayyana a jiya Alhamis a hedkwatar yan sandan jihar Rivers yayinda yake zantawa da manema labarai, mutumin mai shekara 39 wanda ya kasance dan karamar hukumar Asari Toru, yace shi daya yake aikinsa ba tare da kowace kungiya ba.

Yayinda yake magana kan dalilinsa na yin kisan kai, yace bai san abunda ke tunzura shi har ya aikata hakan ba.

“Ban san abunda abunda ke haifar mun da haka ba, ban san me ke tunzurani zuwa ga aikata haka ba amma bayan na aikata sai na fara danasani, sai na fara kuka kan dalilin da yasa na aikata haka. Na ma je cocin Lord Chosen Church da ke kusa da Obigbo. Na fada ma faston cewa na kashe mata a otel cewa ko zai iya taimaka mun don ban san abunda ke damuna ba.

KU KARANTA KUMA: Asiri ya tonu: Mutumin da yake daukar karuwai ya kai otel ya kashe, ya bayyana yadda yake yin wannan aika-aika

“Faston ya gayyace ni zuwa wani wa’azi cewa na halarta sannan na hadu da shugabansu cewa zai taimake ni. Na je wa’azin amma ban samu ganin shugaban ba sannan faston yace mun na tafi ba zai iya taimako na ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel