Assha! Bacin rai ya sa wani magidanci kashe surukarsa da kanwar matarsa da jaririn ta

Assha! Bacin rai ya sa wani magidanci kashe surukarsa da kanwar matarsa da jaririn ta

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Edo ta kama wani mutum mai shekaru 44 mai suna Edoghogho Omorogbe kan laifin kashe surukursa, kanwar matarsa da wani jarriri dan watanni shida.

Ya kashe su ne a ranar 10 ga watan Satumba a garin Iguadolor a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabashin Jihar Edo kuma an gano gawarwakin wadanda ya kashe wato Mrs Alice Omorogbe 52, Mrs Blessinf Efe 25 da jaririn ta.

Edoghogho ya ce ya fusata ne ya kashe surukan nasa saboda duk lokacin da ya samu matsala da matarsa su kan dauki hayar matasa domin su lakada masa dukan tsiya.

DUBA WANNAN: An yanke wa tsohon shugaban kasa hukuncin shekaru biyu a gidan yari

"Ni direban tifa ne amma tunda damina ya kama na koma aikin kwadago.

"Na kashe su ne saboda fushi da nayi domin suruka ta ta kan dauki hayan matasa suyi min duka. Ta kan ce ina yi wa mata ta magana. Idan na samu rashin jituwa da mata ta, za ta aiko matasa suyi min duka.

"Ban san cewa adan zai taba jaririn ba. Na tsere bayan da na kashe su. Daga baya na dawo na fadawa mahaifi na abinda na aikata. Ban ga mata ta ba tun bayan da na kashe mahaifiyarta da 'yar uwanta."

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Danmallam Abubabakar ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel