Babu gudu babu ja da baya kan kaddamar da tsarin takaita amfani da takardan naira - CBN

Babu gudu babu ja da baya kan kaddamar da tsarin takaita amfani da takardan naira - CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya a ranar Juma'a ya ce bankin za ta cigaba da kaddamar da shirin takaita amfani da kudin takarda wato 'cashless policy' a yunkurin ta da ke yi na inganta hada-hadar kudi.

Gwamnan bankin, Mista Godwin Emefiele ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan taron kwamitin tsare-tsare na kudi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ya karyata ikirarin da wasu ke yi na cewa tsarin zai kuntatawa 'yan Najeriya inda ya ce kimamin kashe 5 zuwz 10 cikin 100 na masu asusun bankuna ne abin zai shafa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci a Delta

Ya ce muddin ana son tattalin arzikin Najeriya ya inganta kamara na kasashen da suka cigaba, ya zama dole a rungumi tsarin yin kasuwanci ba tare da amfani da kudin takarda ba wurin hada-hadan.

A baya Legit.ng ta ruwaito muku cewa majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeria wato CBN da ya dakatar da sabon tsarin da ya gabatar na takaita tu'amulli da tsabar naira tare da zare wani kaso cikin kudin masu ajiye idan za su cire tsabar kudi sama da N500,000.

A zaman majalisa na ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, majalisar dokokin tace manufar zai yi sanadiyar samun gagarumin ragi a wajen tsawaita ba da rance a bankunan ajiya na Najeriya.

Yan majalisar sun kuma bayyana cewa tsarin zai kawo koma baya kan masu kanana da matsakaitan kasuwanci “wanda sune ginshikin habbakan tattalin arziki.”

Sai babban bankin na kasa ya ce ba rashin fahimtar abinda tsarin ya kunsa ne yasa wasu daga cikin al'umma ba suyi maraba da shi da farko ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel