Ya ci bashin naira miliyan 2.4 don murnar bikin ranar zagayowar haihuwarsa

Ya ci bashin naira miliyan 2.4 don murnar bikin ranar zagayowar haihuwarsa

- Wata kotun majistare da ke jihar Legas ta yankewa wani matashi mai shekaru 22 wata 6 a gidan maza

- Alkalin ya yanke hukuncin ne bayan amsa laifinsa na zuwa kulob ya yi bushasha har ta naira miliyan 2.4 ba tare da ya biya ba

- Saurayin yayi hakan ne don bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa

Wata kotun majistare da ke Ikeja jihar Legas ta yankewa matashi mai shekaru 22 watanni 6 a gidan maza.

Obinna mai shekaru 22 ya ki biyan kudin bikin zagayowar shekararsa da suka yi a wata kulob wanda har ya kai naira miliyan 2.4.

Obinna ya masa laifukansa biyu na tada hankula da kuma karbar kayan kudi ba tare da biya ba.

Mai shari'a A.A. Fashola ya yankewa Obinna hukuncin watanni hudu a gidan yarin Kirikiri ba tare da zabin tara ba.

Tun farko, Dan sandan da ya mikasa gaban kotu, Sajan Michael Unah, ya sanar da kotun cewa wanda ake karar ya aikata laifin ne a ranar 31 ga watan Agusta da karfe 10:00 na dare a wuri mai lamba 113, titin Obafemi Awolowo da ke Ikeja, jihar Legas.

KU KARANTA: 'Yan majalisar wakilai sun nuna fushinsu ga shuwagabannin tsaron kasar nan

Unah ya zargi cewa wanda ake zargin ya debi abokansa zuwa kulob din da abokansa don murnar zagayowar haihuwarsa karo na 22. Obinna da abokansa sun sha giya har ta naira miliyan 2.4 kuma ya ki biya.

Ya kara da cewa, mamallakin kulob din, Success god, ya kai rahoto ofishin 'yan sanda.

Unah ya ce wanda ake zargin ya yi yunkurin tashin hankula a yayin da yaki biyan kudin giyar da suka sha.

Laifin ya ci karo da sashi na 168 da 314 na dokar laifuka a jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel