'Yan majalisar wakilai sun nuna fushinsu ga shuwagabannin tsaron kasar nan

'Yan majalisar wakilai sun nuna fushinsu ga shuwagabannin tsaron kasar nan

- 'Yan majalisar wakilan Najeriya sun nuna fushinsu ga shuwagabannin tsaron kasar nan akan rashin halartar taron majalisar

- 'Yan majalisar wakilan sun gayyaci shuwagabannin tsaron ne don tattauna halin rashin tsaron da kasar nan ke ciki

- Rashin halaratar taron ya nuna rashin ganin girman 'yan majalisar da kuma nuna halin ko in kula da shuwagabannin tsaron suka yi

Majalisar wakilai ta nuna fushinta akan rashin halartar shuwagabannin cibiyoyin tsaro taron da majalisar ta gayyacesu.

Majalisar ta gayyacesu ne don tattauna halin rashin tsaro da kasar nan ke ciki.

Kakain majalisar, Femi Gbajabiamila, wanda ya nuna bacin ransa karara akan rashin amsa gayyatar, ya ce hakan ya nuna shuwagabannin tsaron basu ba wa mahukuntan girmansu kuma ya nuna cewa basu damu da halin rashin tsaron da ke addabar kasar nan ba.

KU KARANTA: Soyayya ruwan zuma: Ya kashe kansa sakamakon rashin nasarar samun soyayyar wata budurwa

Gbajabiamila ya bukaci dage taron zuwa ranar Litinin sannan kuma ya kara da cewa zai kai karar wadanda basu halarta ba ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mataimakin kakakin majalisar, Idris Wase, ya ce hakan tamkar cin zarafi ne ga majalisar.

Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu da babban daraktan DSS, Yusuf Bichi duk sun halarci taron inda sauran suka turo wakilai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel