Next level: Sai mun shafe shekara 40 abubuwa basu dawo daidai ba a Najeriya saboda irin barnar da Buhari yayi a 'yan shekarun nan - Sheikh Gumi

Next level: Sai mun shafe shekara 40 abubuwa basu dawo daidai ba a Najeriya saboda irin barnar da Buhari yayi a 'yan shekarun nan - Sheikh Gumi

- Fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan na garin Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi yayi wata muhimmiyar magana akan shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Malamin ya bayyana cewa irin barnar da shugaban kasar yayi a bangaren tattalin arziki Najeriya sai ta shafe sama da shekara arba'in ba ta dawo daidai ba

- Haka kuma Malamin ya bayyana cewa zaben da aka yi a shekarar 2019 dinnan shine zabe mafi muni da aka taba yi a Najeriya

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmed Mahmud Gumi, ya bayyana zaben da aka yi a Najeriya a shekarar 2019 dinnan da muke ciki a matsayin zabe mafi muni a tarihin Najeriya.

Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wani babban Fasto na garin Jos, Isa El-Buba a gidan shi dake jihar Kaduna jiya Alhamis 19 ga watan Satumbar nan.

Malamin ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau kan mulki a lokacin da ake ganiyar cin hanci da rashawa, inda ya nuna cewa yana yaki da shi ne.

KU KARANTA: Kowa yaki jin bari zai ji ho-ho: Na yi dana sanin auren 'Slay Queen' a rayuwata - Wani mutumi ya koka

A cewar Sheikh Ahmad Gumi, Najeriya sai ta shafe sama da shekara arba'in kafin ta dawo daidai daga irin barnar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa tattalin arziki.

Haka shima Fasto El-Buba ya yabawa fitaccen Malamin addinin Musuluncin akan jajircewar da yake yi akan gaskiya. Ya kuma kara da cewa abubuwa sun riga sun gama lalacewa a arewacin Najeriya, dan haka yanzu lokaci ne da ya kamata a tsaya a gina yankin arewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel