Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya sun yi ma kwamandojin Boko Haram 7 kisan kiyashi

Nasara daga Allah: Sojojin Najeriya sun yi ma kwamandojin Boko Haram 7 kisan kiyashi

Dakarun rundunar Sojan Najeriya da tare da hadin gwiwar Sojojin hadaka na kasashen dake makwabtaka da yankin Chadi, MNJTF, sun samu nasarar kassara kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a wani samame da suka kai musu a yankin tafkin Chadi.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan kasa, Kanal Sagir Musa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 20 ga watan Satumba, inda yace Sojoji sun kaddamar da samamen ne a sansanin Boko Haram dake garin Tumbus a yankin tafkin Chadi.

KU KARANTA: Murnar cikar Katsina shekaru 32: Jama’an Daura sun nemi a basu takarar gwamna

Sagir yace sun samu sahihan bayanai dake nuna cewa a lokacin da Sojojin suka diran ma yan ta’addan, yan ta’addan suna hanyarsu ta tserewa ne zuwa yankunan kasar Sudan da kasar Afirka ta tsakiya don neman mafaka, kuma Sojoji sun kashe manyan kwamandojinsu guda 7.

Kwamandojin kungiyar Boko Haram guda 7 da aka kashe sun hada da; Abba Mainok, Bukar Dunokaube, Abu kololo, Abor Kime (Balarabe ne daga kungiyar ta’addanci ta duniya-ISIS), Mann Chari, Dawoud Abdoulaye (daga kasar Mali) da kuma Abu Hamza.

“Duka wadannan kwamandojin yan ta’adda ne a yankin Tumbus kafin su gamu da fushin dakarun Soji, koda yake sunayen nan ka iya zama inkiya, amma babbar nasara ce a yaki da ta’addanci a wannan yanki, amma muna cigaba da kokarin gani cikakken bayanansu.” Inji shi

Daga karshe shugaban hafsoshin rundunar Sojan kasa ta Najeriya, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya jinjina ma Sojojin bisa jarumtar da suka nuna a wannan samame, sa’annan ya nemi ya kara zage damtse.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel