Najeriya na kashe biliyan $1.2 duk shekara domin shigo da kifi – CBN

Najeriya na kashe biliyan $1.2 duk shekara domin shigo da kifi – CBN

Gwamnan babban bankin Najeriya wato CBN, Godwin Emefiele ya ce Najeriya na kashe makudan kudin da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 1.2 a ko wace shekara domin shigowa da kifi.

Emefiele ya fadi wannan maganar ne ranar Alhamis 19 ga watan Satumba, 2019 yayin da yake zantawa da wasu Gwamnonin jihohin Najeriya, inda yake basu bayani game da irin nasarar da aka samu a bangaren noma.

KU KARANTA:Gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun raba biliyan N720.880 na watan Agusta 2019

Shugaban bankin, yayi jawabi game da yadda kasuwar kifi ke dada karuwa. A halin yanzu abinda ake iya samu a kasuwanni shi ne ton dubu 800 yayin da bukatar jama’a kuwa take a kan ton miliyan 2.7.

Ya kara da cewa, bukatar babban bankin a nan ita ce fito da shirin hadin gwiwa da gwamnonin jihohin dake makwabtaka da ruwa domin rage kashe kudin da ake yi wurin shigowa da kifin.

A cewar Emefiele, yin amfani da wannan shirin zai habbaka tattalin arzikin jihohin da abin ya shafa kana kuma wata hanya ce ta samawa jama’arta ayyuka daban-daban.

Haka kuma a wani zance mai kama da wannan, shugaban CBN yayi magana a kan shirin hadin gwiwa tsakanin bankin da jami’o’i guda sha biyu na kasar nan.

Manufar shirin kuwa ita ce bunkasa kiwo tsuntsaye domin samar da aikin yi da kuma karin kudin shiga ga jami’o’in. Daga cikin jami’o’in da wannan sabon shirin zai kunsa akwai Jami’ar Ahamdu Bello ta Zariya, Jami’ar harkokin Noma ta gwamnatin tarayya dake Abeokuta, Jami’ar Fatakwal, Jami’ar Najeriya dake Nsukka da kuma Jami’ar Ilorin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel