Da duminsa: Kotu ta tabbatarwa Ikpeazu nasararsa a matsayin gwamnan jihar Abia

Da duminsa: Kotu ta tabbatarwa Ikpeazu nasararsa a matsayin gwamnan jihar Abia

- Gwamna Okezie Ikpeazu na jam'iyyar PDP ya yi nasara a kotun sauraron kararrakin zabe

- Dukkan alkalan sun amince cewa Alex Otti na jam'iyyar APGA da ya shigar da kara ya gaza gabatar da hujoji da ke nuna anyi magudi yayin zaben

- Hakan yasa kotun tayi fatali da kararsa kuma ta jadada Ikpeazu a matsayin zababben gwamnan jihar

Kotun sauraron karrakin zaben gwamna da ke zamanta a Umuahia a ranar Juma'a ta jadada nasarar Okezie Ikpeazu na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin hallastaccen zababen gwamnan jihar Abia.

Channels Television ta ruwaito cewa kotun kuma tayi watsi da karar da Alex Otti na jam'iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA) ya shigar a gabanta na kallubalantar nasarar Ikpeazu.

DUBA WANNAN: Matar aure da nemi kotu ta raba aurenta saboda mijinta baya sallah

Yayin yanke hukuncin, jagoran alkalan kotun mai shari'a Lekan Ogumonye ya bayyana cewa wanda ya shigar da karar ya gaza gamsar da kotun cewa anyi zabe fiye da ka'ida da kuma saba wasu dokokin zabe kamar yadda ya yi zargi.

Hakan yasa dukkan alkalan suka amince da hukuncin watsi da karar tare da jadada nasarar Ikpeazu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel