Kaico: Ma'aikacin Facebook ya kashe kansa a hedkwatan kamfanin

Kaico: Ma'aikacin Facebook ya kashe kansa a hedkwatan kamfanin

Wani ma'aikacin kamfanin Facebook ya rasu sakamakon kashe kansa da ya yi a safiyar ranar Alhamis kamar yadda 'yan sandan Menlo Park suka ruwaito kuma kamfanin ya tabbatar.

The Punch ta ruwaito cewa an jiyo mai magana da yawun kamfanin Facebook yana fadawa kafafen yada labarai na Intanet cewa, "muna cikin bakin ciki sakamakon labarin da muka samu na cew wani ma'aikacin mu ya mutu a hedkwatan mu da ke Menlo Park."

Ma'aikacin ya rasu nan take kusa da rukunin gidajen Jefferson Drive a ginin ofishin Facebook da ke Menlo Park.

Binciken farko da 'yan sanda suka gudanar sun ce babu alamar cewa wani na da hannu cikin mutuwar ma'aikacin.

DUBA WANNAN: Hari kan gidajen mai: Iran tayi martani kan sabbin takunkumin da Amurka ta saka mata

"Yan sandan Menlo Park da jami'an kwana-kwanan na yankin sun ce a lokacin da suka isa wurin sun tarar da wanda abin ya faru dashi a mace," a cewar wata sanarwa da 'yan sandan suka fitar.

Mai magana da yawun Facebook ya kara da cewa, "muna bawa 'yan sanda hadin kai kan binciken da suke gudanarwa kuma muna karfafawa ma'aikatan mu gwiwa.

"Tunda an sanar da iyalansa, a halin yanzu ba bu wani abu da zamu kara cewa a kan batun.

"Muna fatan za mu sanar da al'umma abinda ke faruwa da zarar jami'an tsaro sun yi mana karin bayani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel