Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci a Delta

Yanzu-yanzu: Dauke wutan lantarki ya hana kotun zaben gwamna yanke hukunci a Delta

Kotun sauraron karrarkin zaben gwamna a jihar Delta da ke zamanta a Asaba babban birnin jihar ta jinkirta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar saboda dauke wutan lantarki kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Shugaban alkalan kotun uku, Mai Shari'a Sulaiman Belgore ya jinkirta na dan wani lokaci rike da hankici a hannunsa yana share gumi a fuskansa inda ya ce kotun ba za ta iya cigaba da zamanta ba saboda zafi bayan dauke wutan lantarki.

"Kuyi hakuri, ba za mu iya cigaba a wannan yanayin zafin ba, kotun za ta huta ta dawo bayan mintuna goma."

DUBA WANNAN: Hari kan gidajen mai: Iran tayi martani kan sabbin takunkumin da Amurka ta saka mata

Dan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress, (APC), Great Ogboru ya shigar da kara mai lamba EPT/DT/GOV/01/2019 inda ya ke kallubalantar sake zaben Ifeanyi Okowa na jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) da aka sanar a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 9 ga watan Maris na 2019 da Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta gudanar.

Kotun sauraron karrakin zaben ta tsayar da ranar Juma'a 20 ga watan Satumba a matsayin ranar da za ta yanke hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel