Najeriya za ta kashe naira biliyan 100 a sabon shirinta game da kiwon dabbobi

Najeriya za ta kashe naira biliyan 100 a sabon shirinta game da kiwon dabbobi

Gwamnatin Najeriya ta amince da shirin kawo sauyi a bagaren kiwon dabbobi. A cewar gwamnatin tarayya, ta kafa shirin ne ba wai don shanaye ba kawai, sai don abunda ya shafi kiwon kowani irin dabba a bangaren ma'aikatar kiwon dabbobi a kasar.

A karkashin shirin, za a kashe naira biliyan 100, inda Gwamnatin Tarayya zata ba da kashi 80 na kudin yayin da jihohi za su bada gudumuwar filaye, tsare-tsaren aiwatar da ayyukan, jami'ai da kuma kashi 20 na kudin kafa shirin.

Shirin zai cigaba da kasancewa ga gwamnatocin jihohin dake da ra'ayin shiga tsarin.

Gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi ne bayyana haka a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, bayan taron majalisar tattalin arziki da aka yi a Abuja.

Mista Umahi ne ke jagorantar wani sashin kwamiti akan rigingimu tsakanin makiyaya da manoma.

KU KARANTA KUMA: Jihar Kogi ta gina kamfanin sarrafa shinkafa na biliyoyin naira

A wani labarin kuma mun ji cewa, Hajiya Baheejah Mahmood wanda ita ce shugaban mata na kungiyar nan ta Fulani watau Miyetti Allah na reshen jihar Bauchi ta yi wata hira da ‘yan jaridar Tribune a karshen makon nan.

A wannan tattaunawa da aka yi da Baheejah Mahmood, ta fito ta yi magana game da Makiyaya, shirin RUGA, kiwon dabbobi, da sauran abubuwan da su ka shafi Fulani da ke Najeriya gaba daya.

Jagorarar da kungiyar Miyetti Allah Kautal Hor ta fadawa ‘yan jarida cewa Makiyaya Fulani su na cikin masu taimakawa tattalin arzikin Najeriya, kuma sun taimaka wajen arahar nama da nono.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel