Oyo-Ita: Jami'an tsaro sun mamaye harabar ofishin shugaban ma'aikatan tarayya

Oyo-Ita: Jami'an tsaro sun mamaye harabar ofishin shugaban ma'aikatan tarayya

- Kasa da sa'o'i 12 bayan maye gurbin Oyo-Ita da Yemi-Esan an gano cewa jami'an tsaro sun zagaye harabar ofishin

- Jami'an tsaron sun tsananta bincike ga ma'aikatan ofishin har da baki masu shige da fice

- BMO ta ce hukuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari na nuna cewa babu wanda zai kubuta daga yaki da rashawar da shugaban yasa gaba

A ranar Alhamis, jami'an tsaro suka zagaye ofishin shugaban ma'aikatan tarayya. Kasa da sa'o'i 12 bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci tsohuwar shugabar ma'aikatar, Winifred Oyo-Ita da ta bar aiki.

A ranar Labara ne Buhari ya umarci babbar sakatariyar ma'aikatar albarkatun man fetur, Folashade Yemi-Esan da ta maya gurbin Oyo-Ita don bata damar fuskantar zargin da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ke mata.

Wakilin jaridar Punch ya gano cewa jami'an tsaro sun kewaye ofishin a ranar Alhamis.

Ofishin na nan a cikin sakatariyar tarayya, kashi na II a titin Shehu Shagari da ke babban birnin tarayya Abuja.

Jami'an tsaron sun bukaci duk ma'aikatan ofishin da su sagale katin shaidarsu na aiki don ganesu da wuri don samun shiga harabar ofishin.

KU KARANTA: Soyayya ruwan zuma: Ya kashe kansa sakamakon rashin nasarar samun soyayyar wata budurwa

Ba kamar da ba, ma'aikatan ofishin da baki na yin amfani da kofa guda ne don shiga amma a ranar Alhamis an bukaci baki da yin amfani da kofa 5, sai ma'aikatan su yi amfani da sauran kofofin.

Bayan bayyana kanka da dalilin ziyara, bakin suna rubuta sunansu, lambar waya, ofishin da aka zo ziyarta da kuma lokacin da aka iso.

Yayin barin harabar, ana bukatar bakin da su sa hannu shaidar sun fice daga harabar.

A ziyarar karshe da wakilin Punch ya kai, duk babu wadannan tsare-tsaren.

Idan zamu tuna, jaridar Punch ta ruwaito cewa halin da sakateriyar tarayyar take ciki na rashin tsafta da kula ya kazanta.

A jiya kuwa an gano cewa gyare-gyare, share-share da goge-goge sun yawaita a cikin sakateriyar.

A maida martanjn da kungiyar yada labarai ta Buhari ta yi akan maye gurbin Oyo-Ita, kungiyar ta ce hakan na nuna cewa yaki da rashawa na shugaban kasar bai zai wuce kowa ba, sai wanda ba ruwansa.

Kamar yadda kungiyar ta sanar, sauke Oyo-Ita wata alama ce da ke nuna cewa gwamnatin Buhari ba za ta bar mutanen da ake zargi da wata badakala a ofishinsu ba.

Kungiyar ta ce hakan na nunawa masu mukami a gwamnatin Buhari ne cewa ba fa zasu tafi haka ba matukar suka bayyana wani hali na zargi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel