Jihar Kogi ta gina kamfanin sarrafa shinkafa na biliyoyin naira

Jihar Kogi ta gina kamfanin sarrafa shinkafa na biliyoyin naira

Gwamnatin jihar Kogi ta bayyana cewar ta kashe aira biliyan hudu domin gina kamfanin sarrafa shinkafa a jihar wanda ke iya samar da ton 50 na shinkafa a kullun.

Gwamnan jihar Yahaya Bello ne ya bayyana hakan a wata ziyarar gani da ido da ya kai kamfanin wanda aka gina a kusa da dam din Omi da ke kauyen Ejiba na karamar hukumar Yagba ta yamma.

A cewar Bello, masana’antar za ta dauki akalla ma’aikata guda 500 sannan kuma a kowani wata za a samu kudin shiga a asusun jihar da yakai naira miliyan 300, cewa hakan zai taimaka wa gwamnati matuka wajen samun karin kudaden shiga.

Yace: “Baya ga shinkafa kamfanin za ta rika sarrafa abincin kifi da kaji domin akwai akalla mutane masu manyan gidajen kiwon kifi sama da 500 a jihar.”

Bayan haka gwamna Bello ya ce gwamnati ta gina kamfanin samar da wutar lantarki da zai iya samar da wuta har wat 500.

KU KARANTA KUMA: Toh fah: Kungiyar CAN ta zargi El-Rufai da shirin rushe wata babbar coci mafi tsufa a Zaria

“A lissafin da muka yi masana’antar ita kanta za tayi amfani da wat 200 sannan sauran 300 za mu raba wa gidajen dake kusa da dam din.”

Daga karshe gwamnan yace yana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kadamar da wannan kamfani kafin lokacin zaben gwamnan jihar wato ranar 16 ga watan Nuwamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel