Toh fah: Kungiyar CAN ta zargi El-Rufai da shirin rushe wata babbar coci mafi tsufa a Zaria

Toh fah: Kungiyar CAN ta zargi El-Rufai da shirin rushe wata babbar coci mafi tsufa a Zaria

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, ta koka kan zargin cewa ana shirin rushe cocin Anglican mafi tsufa a Zaria, biyo bayan takardar sallama da gwamnatin jihar ta bayar.

Don haka kungiyar CAN, ta ja hankalin Gwamna Nasir El-Rufai zuwa ga takardar arin wuri na kwanaki bakwai da hukumar kula da ci gaban birane ta jihar Kaduna wato KASUPDA ta bayar ka rushe cocin Saint George’s Anglican Church a Sabon Gari, Zaria, wanda aka gina kimanin shekaru 110 da suka gabata.

A wani jawabi daga Shugaban kungiyar CAN, Reverend Joseph Hayab a jiya Alhamis, 19 ga watan Satumba, ya bayyana cewa ance takardar tashin umurni ne daga Gwamna El-Rufai.

“Takardar sallaman mara dauke da kwanan wata, zuwa ga: Gida mai lamba 27, Church House, kasuwar Sabon Gari, Zaria, wanda ya kasance gidan St George’s Church, har ila yau an yi ikirarin cewa an biya diyya ga cocin.

“Kamar yadda umurni gwamna ya zo akan lamari bunkasa kasuwa wanda aka biya diyya. Don haka, ana umurtan ku da ku bar gidan cikin kwanaki bakwai daga yanzu, rashin bayar da hadin kai zai sa hukumar ta tsige ku ta karfin tuwo,” kamar yadda yake kunshe a takardar.

Sai dai, CAN ta kuma bayyana cewa sa hannun da ke dauke a takardar bai sanya sunansa ba, maimakon haka yana dauke ne da sa hannun Shugaban KASUPDA a madadin manajan yankin: “Muna kokwato akan haka, ko da gaske ne cewa umurnin ya fito ne daga gwamnan, amma muna tantama sosai akan ko gwamnan zai bayar da wannan umurnin.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Limami ya bayyana yadda wata karuwa da ya hadu da ita tayi kokarin yi masa fyade

“Hakan ya kasance ne saboda a watan Fabrairunn 2016, gwamnatin jihar tayi yunkurin sauya wa cocin waje domin samun dammar habbaka kasuwan, amma daga bisani sai ta gane cewa cocin na da duk wasu takardu da ake bukata harma wasu bangare na kasuwan ya shiga filin cocin.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel