Nnamdi Kanu ya bukaci UN ta sa baki don sakin Sawore da El-Zakzaky

Nnamdi Kanu ya bukaci UN ta sa baki don sakin Sawore da El-Zakzaky

- Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya bukaci majalisar dinkin duniya da ta sanya baki don sakin Omoyele Sowore da Sheikh El-Zakzaky

- Kanu ya yi kiran ne a yayin taron da yayi da bangarori da kuma cibiyoyin majalisar dinkin duniya

- An tattauna matsalolin da mutanen kasar nan ke fuskanta na take hakkokinsu da ake yi, in ji Sakataren yada labarai na IPOB

Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, ya bukaci majalisar dinkin duniya da ta umarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da sakin Omoyele Sowore da Sheikh El-Zakzaky.

Sakataren yada labarai na IPOB, Emma Powerful, ya ce bukatar na daga cikin zantukan da Kanu ya tattauna a taron da ya yi da cibiyoyin majalisar dinkin duniyar kwanan nan.

Powerful ya kara da cewa, sun tattauna akan gurin kiwo na makiyaya wanda aka sani da Ruga a taron.

Ya ce, kokarin Kanu na ganin samun yancin mutanensa ya wuce a Najeriya kadai, ya mika bukatar hakan ga bangarori da cibiyoyi na majalisar dinkin duniya.

Ya ce, "Ba za a cigaba da kyale matsalar Biafra ba; ta kai matakin duniya."

Ya ce Kanu ya bukaci matakin gaggawa akan hakkokin mutane da ake takewa da kuma tallafi akan hakkokin mutanen Biafra da ake takewa.

Takardar ta ce, "Kowacce matsala da ke damun mutanenmu a halin yanzu tana gaban bangarori da cibiyoyin majalisar dinkin duniya. Ba za a cigaba da nuna halin ko in kula ga matsalarmu ba. An daga maganar RUGS a taron."

"Kisan gillar da 'yan ta'addan Fulani makiyaya ke wa 'yan Biafra da kuma kashe 'yan yankin da sojoji da 'yan sandan Najeriya ke yi duk an tattauna."

Powerful ya ce, Kanu ya samu rakiyar mataimakinsa, Uche Mefor, Mazi Chika da sauransu zuwa majalisar dinkin duniyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel