Gwamnatin Najeriya na kokarin karbar bashin dala bilyan 2.5 daga bankin duniya

Gwamnatin Najeriya na kokarin karbar bashin dala bilyan 2.5 daga bankin duniya

- Gwamnatin tarayyar Najeriya na yunkurin karbar bashin $2.5bn daga bankin duniya

- Mataimakin shugaban bankin na nahiyar Afirka, Hafez Ghanem ne ya bayyana hakan

- Dama dai tuni Najeriya na da bashin $2.4bn yanzu kuma take neman karin $2.5bn daga bankin duniya

A halin yanzu, gwamnatin tarayya na tattauna yadda zata karbi sabon bashin $2.5bn da bankin duniya.

Mataimakin shugaban bankin na Afirka, Hafez Ghanem ne ya bayyana hakan a tattaunar da aka yi da shi a garin Abuja, jaridar Bloomberg ta ruwaito.

A shekarun da suka gabata, Najeriya ta karbi bashin $2.4bn daga bankin duniyan in ji Ghanem.

"A yanzu haka muna tattauna sabon bashin da Najeriya ke so na $2.5bn," in ji shi.

"Shawo matsalar wutar lantarki a Najeriya yana da matukar amfani saboda hakan ne zai jawo masu saka hannayen jari don cigaban habakar tattalin arzikin Najeriya,"

Bashin cikin gida na Najeriya ya kai $55.6bn inda bashin waje ya kai $25.6bn.

Idan zamu tuna, babu dadewa ministar kudi, kasafi da tsari na kasa, Zainab Ahmed, ta ce Najeriya ba ta da matsalar bashi duk da maganganun masana tattalin arziki akan hauhawar bashin kasar nan.

KU KARANTA: Sanwo-Olu ya yi wa 'yan Najeriya da suka dawo daga kasar Afirka ta kudu kyauta

Banda bashi, ministar ta ce babbar matsalar kasar itace kudin shiga. Ta kara da zargar masu kalubalantar karbar bashin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da 'rashin damuwa da halin da kasar ke ciki'.

Ahmed ta ce, bashin Najeriya bai yi yawa ba, babbar matsalar kasar nan shi ne kudin shiga.

"Bashinmu har yanzu bai yi yawa ba. A takaice, a cikin kasahe sa'o'inmu muna cikin masu karancin bashi."

Amma kuma ta ja kunnen cewa Najeriya zata wahala matukar ba a habaka yanayin kudin shigar kasar ba.

Ministar ta ce gwamnatin tarayya na da burin daga kudin shiga daga 55% na 2018 zuwa 85% a shekaru 4 masu zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel