An yanke wa tsohon shugaban kasar El Salvador hukuncin shekaru biyu a gidan yari

An yanke wa tsohon shugaban kasar El Salvador hukuncin shekaru biyu a gidan yari

Ofishin alkalin alkalai na kasar El Salvador ta yanke wa tsohon shugaban kasar Antonio Saca hukuncin shekaru biyu a gidan yari bayan samunsa da laifin cin hanci.

The Punch ta ruwaito cewa kotun ta samu tsohon shugaban mai shekaru 54 da laifin yunkurin bawa wani ma'aikacin kotu cin hanci na dalla 10,000 domin ya binciko masa wasu bayannai kan wata shar'ar tuhumar rashawa da ake yi a kansa kamar yadda La Prensa Grafica ta wallafa.

Saca, wanda ya shugabanci kasar daga 2004 zuwa 2009, "ya amsa laifin da ake tuhumsa da aikatawa" kamar yadda ofishin alkalin alkalai na kasar ta bayyana a Twitter.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun rufe ofishin O'Pay a Kano

Dama tsohon shugaban kasar yana gidan yari bayan an yanke masa hukuncin shekaru 10 bayan samunsa da laifin almubazarranci da dukiyar al'ummar har dala miliyan 300 da kuma laifin karkatar da kudade.

Lauyan mai yaki da rashawa ya shaidawa manema labarai cewa a halin yanzu alkali bai fadi yadda tsohon shugaban kasar zai yi karin shekaru biyu da aka yanke masa ba.

Hakan na nufin akwai yiwuwar shekaru biyun na iya cigaba lokaci guda da hukuncin shekaru 10 da aka yanke masa tun a baya ko kuma kotun ta kara masa sabon wa'adi na shekaru biyun wadda hakan na nufin zai yi shekaru 12 a gidan yari kenan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel