Ga irin ta nan ai: Wani mutumi ya yiwa matar shi yankan rago bayan ya gano cewa 'ya'yan da ta haifa mishi guda 6 duk ba na shi bane

Ga irin ta nan ai: Wani mutumi ya yiwa matar shi yankan rago bayan ya gano cewa 'ya'yan da ta haifa mishi guda 6 duk ba na shi bane

- Wani mutumi ya yiwa matarsa yankan rago bayan ya gano cewa 'ya'yan da ya kwashe rayuwarsa yana wahala da su ba nashi bane

- Mutumin ya samu likitoci ne sun binciko masa DNA na shi dana 'ya'yan nasu guda shida, inda suka bayyana masa cewa ko daya a ciki babu na shi

- Ya kara da cewa abinda yafi bata masa rai shine yadda take takura masa da karbar kudi akan wahalar yaran bayan ta san ba 'ya'yan shi bane

Wani rahoto da muka samu ya nuna, Karen Rainford, matar da take da 'ya'ya shida ta gamu da ajalinta a Mountain View a shekarar 2014, inda mijinta da suka jima suna zaman aure tare yayi mata yankan rago.

Majiya mai karfi ta bayyana cewa mutumin mai suna Rainford ya sanar da cewa 'ya'yan da ya kwashe shekaru yana rainon su duka babu ko guda daya da yake na shi.

Kwana daya kafin yayi wannaan aika-aikar, mutumin bayan ya gano gaskiyar lamarin ta hanyar gwajin da yaje likitoci suka yi na DNA, sun bayyana masa cewa ko daya a cikin 'ya'yan babu na shi, inda shi kuma bayan ya dawo gida yake sanar da mutane cewa sai ya kashe ta.

KU KARANTA: Tirkashi: 'Yan sanda zasu kama duk wani matashi da suka gani yana rike da wayar iPhone 11 daga nan zuwa Disamba

Mutanen da suke makwabtaka da su sun bayyana cewa, matar tana yawan zuwa wajen aikin mijin nata ta tambayeshi ya bata kudin da zata dauki nauyin 'ya'yan na su.

Ya bayyana cewa abinda yafi bashi haushi kenan, yadda take bin shi tana karbar kudi a wajen shi, bayan ta san cewa 'ya'yan ba na shi bane, ya kara da cewa wannan dalilin ne ya sanya ya kashe ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel