Gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun raba biliyan N720.880 na watan Agusta 2019

Gwamnatocin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun raba biliyan N720.880 na watan Agusta 2019

Kwamitin kula da tallafin kudi da kuma asusun tarayyar Najeriya wato FAAC a ranar Alhamis 19 ga watan Satumba bayan kammala zamansa karkashin jagorancin Ahmed Idris babban mai kula da asusun tarayya ya raba kudin wata Agusta 2019.

Adadi kudin da aka kasafta a tsakanin gwamnatin tarayya, ta jihohi da kuma kananan hukumomi shi ne biliyan N720.880 na watan da ya gabata wato Agusta.

KU KARANTA:‘Yan sanda sun kama wani fitinanne mai kisan mutane a jihar Rivers (Hotuna)

Wannan kudin da an samo shi ne daga kudade shiga, harajin kayayyakin amfani wato VAT da kuma cinikayya tsakanin kasa da kasa.

Abinda aka samu gaba daya na watan Agustan shi ne N631.796b, wanda ya ragu da biliyan N42.569 daga cikin abinda aka samu a watan da ya gabace shi.

Har wa yau, kudin shiga da aka samu daga harajin kayayyakin amfani ya kama biliyan N88.082 wanda yayi kasa da biliyan N94.159 daga abinda aka samu a watan da ya gabace sa.

Wata majiya dake da kusanci ga wannan kwamiti ta sanar damu cewa, daga cikin biliyan N720.880 gwamnatin tarayya ta samu biliyan N301.804 inda jihohi suka samu biliyan N188.925 yayin da kananan hukumomi suka tashi da biliyan N142.654.

Haka zalika a wani labarin kuwa, zaku ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta samu nasarar damke wani hatsbibin mai kisan mutane a ranar Alhamis 19 ga watan Satumba.

Rahotanni sun bayyana mana cewa matashin mai suna David West ya shiga hannun hukuma ne a lokacin da yake kokari barin Fatakwal zuwa birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel