Jama’a sun koma ga shinkafa yar gida bayan tashin farashin shinkafa yar waje wanda buhu ya koma N20,000 a yanzu

Jama’a sun koma ga shinkafa yar gida bayan tashin farashin shinkafa yar waje wanda buhu ya koma N20,000 a yanzu

Farashin shinkafa yar waje yayi tashin gwauron zabi yayinda mutanen Enugu suka koma neman shinkafa yar gida ido rufe biyo bayan rufe iyakokin Benin da Nijar da gwamnatin tarayya tayi.

Wani binciken farashin kayayyaki a kasuwa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) tayi a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba ya bayyana cewa mazauna jihar da dama sun koma ga shinkafa yar gida sakamakon hawa da farashin shinkafa yar gida yayi.

NAN ta ruwaito cewa farashin shinfaka yar waje a kasuwannin Akwata, Ogbete, Garki da Mayor ya tashi inda buhun shinkafa yar 50kg na waje ya ke a tsakanin N19,500 da N20,000 sabanin yadda yake a watannin baya kan N17,500.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: An gurfanar da wata uwargida kan daukar mijinta hoto ba tare da izininsa ba

Binciken ya kuma nuna cewa a yanzu ana siyar da karamar buhun shinkafa yar 25kg na waje tsakanin N9,000 da N9,500 sabanin yadda take a baya kan N8,000 da N9,000.

Dilallan shinkafa yar waje, wadanda suka zanta da NAN a manyan kasuwanni daban-daban na birnin, sun daura alhakin hauhawan farashin kan rufe iyakar kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel