Imo: 'Yan sanda suna neman wani gawurataccen dan fashi da makami ruwa a jallo

Imo: 'Yan sanda suna neman wani gawurataccen dan fashi da makami ruwa a jallo

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Imo ta sanar da cewa tana neman wani gawurtaccen dan fashi da makami mai suna Ebuka Ukachukwu da wasu ke yi wa lakabi da 'small witch'.

Daily Trust ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Ikeokwu Godson Orlando ya ce ana neman Ukachukwu ne saboda zarginsa da hannu cikin aikata wani fashi da makami.

A sanarwar da rundunar da fitar a birnin Owerri a ranar Alhamis, Kakakin 'yan sandan ya ce, "ana kuma nemansa saboda laifukan mallakar bindigu ba bisa ka'ida ba, shiga kungiyar asiri da ayyukan kungiyar na asiri.

DUBA WANNAN: An bayyana yadda 'yan bindiga suka bi wani basaraken arewa har gida suka kashe shi

"Ebuka Ukachukwu da wasu ke kira 'small witch' matashi ne mai shekaru 22 a duniya kuma dan asalin kauyen Abatu a karamar hukumar Oguta na jihar. Za a cigaba nemansa ruwa a jallo har sai an kama shi."

SP Ikeokwu ya bukaci al'umma su taimakawa rundunar da bayyanai masu muhimmanci da zai iya taimakawa wurin gano inda ya ke domin a kama shi.

A wani rahoton, Legit.ng ta kawo muku cewa a ranar Alhamis 19 ga watan Satumban 2019 ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta samu nasarar damke kasurgumin mai kisan mutanen nan, Gracious David a jihar Rivers.

'Yan sandan sun kama David ne a kan hayarsa ta zuwa Uyo

David daya ne daga cikin ‘yan kungiyar asiri ta Degbam. Kuma daga lokacin da aka kama shi zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan ta ce ya sanar da ita bayanai masu matukar amfani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel