Zaben gwamnan Kogi: PDP ta gargadi INEC da Bello kan rikici da magudi

Zaben gwamnan Kogi: PDP ta gargadi INEC da Bello kan rikici da magudi

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, ta gargadi hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da kada tayi yunkurin fakewa da rikici wajen yin magudi a zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba, a jihar Kogi.

A Wani jawabi daga hannun babban sakatarenta na kasa, Mista Kola Ologbondiyan zuwa ga manema labarai a Abuja, jam’iyyar ta kaddamar da cewa tana da tabbacin lashe zaben Kogi sannan kuma cewa ya zama dole INEC ta tabbatar da gudanarwa na gaskiya, cewa rashin hakan ne ke haifar da hanzuga da rikici a zabe.

Ta nace kan cewa ya zama dole INEC ta isar da gargadi kai tsaye zuwa ga gwamnan jihar Yahaya Bello da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin su janye daga kowani irin rikici a zaben, domin cewarta a shirye mutanen Kogi suke sannan sun shirya tunkarar gwamnan da jam’iyyarsa gaba-da-gaba.

KU KARANTA KUMA: Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin Sokoto yayi nasara a kotun zabe

Jam’iyyar ta tunatar da INEC da Yahaya Bello da su lura cewa mutane za su yi gangami ne a zaben ranar 16 ga watan Nuwamba, domin juya baya ga gwamnatin rashin adalci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel