Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Jakadar kasar Jamus, Birgitt Ory

Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Jakadar kasar Jamus, Birgitt Ory

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a Abuja ya ce Najeriya tana maraba da masu son saka hannun jari a fanin ayyuka musamman fanin samar da wutan lantarki da zai haskaka gidajensu da inganta kasuwancin su.

The Punch ta ruwaito cewa shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne yayin ganawarsa da jakadar kasar Jamus a Najeriya, Birgitt Ory lokacin da ta zo mika masa wasikar kama aiki inda ya ce gwamnatin Najeriya ba za ta saba yarjejeniyar kwangila ba idan kamfanonin Jamus suna sha'awan saka hannun jari a kasar.

Kamar yadda ya ke dauke cikin wani sako da hadimin shugaban kasa Buhari Sallau ya fitar dauke da sa hannun mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina, Shugaban kasar ya ce 'yan Najeriya sunyi maraba da kwangilar da aka rattabu hannu kai tare da kamfanin Siemens na Jamus inda ya ke fatan kasashen biyu za su amfana da kwangilar.

DUBA WANNAN: An bayyana yadda 'yan bindiga suka bi wani basaraken arewa har gida suka kashe shi

Buhari ya ce Najeriya tana godiya bisa taimakon da Jamus ke bawa 'yan Najeriya a matsayin tallafi na mutanen da suka rasa muhallansu a yankin Arewa maso Gabas da ziyarar da shugaban Jamus, Angela Merkel ta kai Najeriya a Augustan 2018 na kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

A jawabin ta, jakadar na Jamus ta ce tayi matukar farin cikin samun daman yin aiki a Najeriya duba da cewa ta dade tana burin afkuwar hakan.

Ta ce Najeriya ce, "kasa mafi girma da muhimmanci a nahiyar Afirka.

"A lokacin da na zo Najeriya a Mayun bara wanda shine zuwa na na farko Afirka, da fitowa ta daga jirgi sai nace tabbas wannan kasar na ke son inyi aiki," inji ta.

Jakadar da kuma tana Najeriya murnar samun muhimman mukamai a Majalisar Dinkin Duniya inda ta ce hakan alama ce da ke nuna muhimmiyar rawar ta kasar ke takawa a Afirka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel