Abin da Osinbajo ya fada mana a kan sabon kwamitin EAC da Buhari ya kafa - Gwamna Yahaya

Abin da Osinbajo ya fada mana a kan sabon kwamitin EAC da Buhari ya kafa - Gwamna Yahaya

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya ce mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinabjo, ya fada musu cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa sabon kwamitin bashi shawara a kan tattalin arziki ne domin su taimake shi.

Yahaya ya ce Osinbajo ya fada musu hakan ne ranar Alhamis bayan sun nemi karin bayani daga gare shi a kan kafa sabon kwamitin EAC yayin taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) da suka yi a fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya, Abuja.

"Gwamnoni sun nemi karin bayani daga wurin mataimakin shugaban kasa a kan alakar da ke tsakanin NEC da sabon kwamitin EAC da aka kafa.

"Mataimakin shugaban kasa ya bayyana mana cewa EAC kwamiti ne da zai taimaka wa shugaban kasa da shawarwari yayin da kundin tsarin mulkin kasa, shine ya tsara NEC da mambobinsa. Kwamitin biyu zasu yi aiki tare.

DUBA WANNAN: Abin da muka tattauna da shugaba Buhari - Shugabannin hukumomin tsaro

"Ya sanar da mu cewa lokaci zuwa lokaci za a ke sanar da NEC al'amuran kwamitin EAC bisa izinin shugaban kasa," a cewarsa.

A ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da kafa sabon kwamitin da zai ke bashi shawara a kan tattalin arziki.

Batun kafa sabon kwamitin ya jawo cece-kuce da zargin cewa shugaba Buhari na kokarin rage karfin da mataimakinsa ke da shi a cikin gwamnatinsa, musamman ganin cewa Osinbajo ne ke jagorantar kwamitin a baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel