Abin da muka tattauna da shugaba Buhari - Shugabannin hukumomin tsaro

Abin da muka tattauna da shugaba Buhari - Shugabannin hukumomin tsaro

A ranar Alhamis ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya zaburar da shugabannin hukumomin tsaro na kasa da su kawo karshen satar danyen man fetur a Najeriya.

Babban sifeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Mohammed Adamu, ya ce shugaba Buhari ya fada musu hakan ne yayin ganawar sirri da suka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

IGP Adamu, wanda ya yi magana amadadin sauran shugabannin hukumomin tsaro, ya ce shugaban kasa ya bukaci su rubanya tsaro a wuraren da bututun danyen mai suke domin dakile satar man da ake yi.

"Duk da ana samun cigaba ta fuskar tsaro a kasa, shugaban kasa ya bukaci mu tabbatar da an kara samun tsaro a dukkan sassan Najeriya.

"Kazalika, ya zaburar da mu a kan daukan tsaurara matakan tsaron bututun man fetur domin ganin Najeriya ta daina asarar kudin shiga sakamakon satar danyen man fetur," a cewarsa.

DUBA WANNAN: Najeriya ce kasa ta uku a duniya da 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka - Rahoton masana

IGP Adamu ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara ta fuskar raguwar aiyukan ta'addanci, musamman garkuwa da mutane da matsalolin 'yan bindiga da sauran kalubalen tsaro a fadin kasa.

"Za a iya ganin irin cigaban da aka samu a yankin arewa maso yamma da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, an samu raguwar aiyukan ta'addanci sosai, kuma muna da alkaluma da zamu iya kare abinda muka fada," a cewar shugaban na rundunar 'yan sanda.

Kazalika, ya bayyana cewa sun gabatar da irin nasarorin da jami'an tsaro suka samu wajen lalata sansanin 'yan ta'adda, musamman masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga, a hanyar Abuja zuwa Kaduna da yankin Birnin Gwari zuwa jihar Neja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel