Ma'aurata sun hallaka $120,000 da banki ta yi kuskuren tura musu

Ma'aurata sun hallaka $120,000 da banki ta yi kuskuren tura musu

- Wasu ma'aurata a Pennsylvania sun lamushe $120,000 da bankin suka yi kuskuren tura musu cikin asusun bankinsu

- Tuni dai ma'auratan suka hallaka miliyoyi daga cikin kudaden

- A yanzu dai ma'auratan na gurfane a gaban kotu da zargin sata

An zargi wasu ma'aurata da sata sakamakon kashe $120,000 ( N36.7m) da aka yi kuskuren tura musu a asusun bankinsu.

Robert Williams da matarsa, Tiffany Williams sun gurfana a gaban kotu a ranar Talata bayan da suka yi kusan mako biyu da rabi suna watanda da kudaden. Ma'auratan sun siya motoci da sauran ababen more rayuwa.

Robert mai shekaru 36 da matarsa mai shekaru 35 sun gurfana a gaban kotu ne akan laifin sata.

'Yan sanda sun bada rahoton cewa bankin BBT sun tura kudin asusun bankin ma'auratan a bisa kuskure a ranar 31 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Kotu ta yanke hukuncin kwace kadarorin kamfanin P&ID

Amma zuwa ranar 19 ga watan Yuni, sun hallaka miliyoyi daga cikin kudin ta hanyar siyan manyan motoci da sauran ababen more rayuwa. Bayan haka sun barnatar da kudin wajen farantawa abokan arziki.

A ranar 20 ga watan Yuni, bankin sun tuntubi Tiffany akan kuskuren da suka yi tare da sanar dasu cewa an kwashe kusan $107,416 daga cikin kudin.

Jaridar Williamsport Sun-Gazette ta ruwaito cewa Tiffany ta sanar da bankin cewa "Zata yi wa mijinta maganar tare da shirya yadda za a dawo da kudin," inji 'yan sanda.

Amma lokacin da bankin suka gane cewa ma'auratan ba zasu iya biyan kudin ba, sai suka tuntubi hukumomi don tallafin yadda za a dawo da kudaden.

Robert ya tabbatarwa da masu bincike a watan Yuli cewa shi da matarsa sun san ba kudinsu bane amma suka dinga watanda da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel