Tattalin arziki: Dangote ya jinjina ma Buhari game da zabo kwararrun mashawarta

Tattalin arziki: Dangote ya jinjina ma Buhari game da zabo kwararrun mashawarta

Mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, Aliko Dangote ya jinjina ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yadda ya zabo kwararrun mutane a matsayin wadanda za su bashi shawara a kan tattalin arzikin kasa, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dangote ya bayyana mutanen da Buhari ya zabo a matsayin wadanda suka san abinda suke yi, kuma zasu kara ma masu zuba hannun jari kwarin shigowa Najeriya tare da habbaka tattalin arzikin kasar.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Tsohon shugaban kasar Tunisia ya rasu a kasar Saudiyya

Dangote ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi a taron kaddamar da gidan kamfanin hukumar Chemical and Non-Metallic Products Employers Federation, CANMPEF a ranar Alhamis a jahar Legas.

Dangote yace kasuwancinsa na samun gagarumar cigaba sakamakon kyawawan tsare tsare da gwamnati ta bullo dasu, don haka yake kara fadada kasuwancin nasa. “A Najeriya kadai muna iya samar da tan miliyan 29 na siminti, kuma zamu fadadashi zuwa tan 35 a 2020.

“mun taimaka sosai wajen sauya akalar Najeriya daga kasancewa kasa da take shigo da siminti zuwa kasar da take fitar da siminti wasu kasashen duniya, kamfaninmu na siminti ya samar da aiki ga mutane 25,000 a duk fadin kasar nan.” Inji shi.

Da yake tsokaci game da rufe iyakokin Najeriya, Dangote yace lokaci yayi da Najeriya za ta tattauna da kasashen Bini da Nijar domin kuwa bai kamata ta lamunci a cigaba da fasa kaurin kayayyaki zuwa ciki da wajen kasar nan ba.

Daga karshe Dangote ya sharwaci gwamnatin Najeriya da ta gindaya ma kasar Bini sharadin daina bari ana shigo da shinkafa Najeriya idan har tana son a bude iyakar Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel