Yanzu Yanzu: Majalisa ta bukaci CBN ya dakatar da sabon tsarin zaftare kudi daga masu ajiya

Yanzu Yanzu: Majalisa ta bukaci CBN ya dakatar da sabon tsarin zaftare kudi daga masu ajiya

Majalisar wakilai ta bukaci babban bankin Najeria wato CBN da ya dakatar da sabon tsarin da ya gabatar na karban kudi daga kan masu yin manyan ajiya.

A zaman majalisa na ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba, majalisar dokokin tace manufar zai yi sanadiyar samun gagarumin ragi a wajen tsawaita ba da rance a bankunan ajiya na Najeriya.

Yan majalisar sun kuma bayyana cewa tsarin zai kawo koma baya kan masu kanana da matsakaitan kasuwanci “wanda sune ginshikin habbakan tattalin arziki.”

A wani jawabi da yayi fice a ranar Talata, babban bankin CBN ya bada sanarwar cewa bankunan da ke karbar ajiya za su rika cire wani kaso na kudin da su ka adanawa jama’a.

An kawo wannan tsari ne domin a rage yawo da tsabar kudi a fadin kasar. Bankunan da ke adana kudin mutane za su rika karbar wani kaso idan mutum zai zare kudi ko zai ajiye.

KU KARANTA KUMA: Mayakan Boko Haram sun fara gudu su na barin Najeriya – Rundunar soji

Yace za a rika zaftare 5% ne idan masu kamfani su ka zo cire tsabar kudi daga banki, kuma za a rika karbar 3% daga hannun su a duk lokacin da su ka kawo kudinsu domin a zuba masu cikin akawun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel