Wani direban tifa ya arce bayan ya kashe mutum 2 a Anambra

Wani direban tifa ya arce bayan ya kashe mutum 2 a Anambra

Wani direban tifa ya hallaka mutum biyu har lahira a shiyyar Mbanakwa dake karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.

Wakilan jaridar Punch ya tabbatar mana da cewa direban ya ranta cikin na kare bayan ya aikata wannan aiki.

KU KARANTA:Mayakan Boko Haram sun fara gudu su na barin Najeriya – Rundunar soji

Rahotanni daga jaridar Punch sun tattaro mana cewa direban yana kokarin hawa wani tsauni ne a lokacin da wannan abu ya faru, sakamakon neman birki da yayi ya rasa kawai sai ya hau kan wadansu mutane biyu.

Wani ganau wanda abin ya faru a kan idonsa ya fada mana an kai mutanen asibiti a lokacin da abin ya faru inda a can asibitin ne rai yayi halinsa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Haruna Muhammad ya tabbatar aukuwar wannan lamarin a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Muhammad ya ce: “Akwai wani hatsarin da ya auku a karamar hukumar Nnewi ta Arewa tsakanin wata tifa mai lamba XA 206 KPP da kuma babur mai lamba QL 500 UWN wanda Clement Odo ke ja dauke da Anayo Elinye.

“A binciken da muka gabatar na farko mun gano cewa tifar ta samu matsalar birki ne a lokacin da take kokarin hawa saman wani tsauni. Wannan ne ma yayi sanadiyar ta gangaro baya inda ta haye saman mutanen biyu dake bisa babur.

“Dukkanin mutanen biyu sun mutu bayan an kai su asibiti a daidai lokacin da abin ya faru. Sai dai kuma direban tifan ya arce, amma muna cigaban da nemansa domin gurfanar da shi a gaban shari’a.” A cewar kakakin ‘yan sandan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel