Soyayya ruwan zuma: Ya kashe kansa sakamakon rashin nasarar samun soyayyar wata budurwa

Soyayya ruwan zuma: Ya kashe kansa sakamakon rashin nasarar samun soyayyar wata budurwa

- Badamasi Musa mai shekaru 35 ya kashe kansa ta hanyar rataya sakamakon rashin nasarar samun soyayyar wata budurwa

- A yammacin ranar Laraba ne mahaifiyarsa ta gansa da igiya, amma sai ya sanar da ita icce zai yi

- Safiyar ranar Alhamis aka tsinci gawarsa sagale a bishiyar mangwaro

A safiyar ranar Alhamis ne aka tsinkayi gawar Badamasi Musa mai shekaru 15 a sagale a bishiyar mangwaro a kauyen Kabomo, karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.

Musa ya kashe kansa ne sakamakon rashin nasarar samun soyayyar wata abar kaunarsa a kauyensu, in ji wata majiya.

Mamacin manomi ne wanda yakan taba kananan kasuwanci.

Ya fusata ne a dalilin rashin nasarar samun soyayyar abar kaunarsa wacce a halin yanzu bamu samu sunanta ba.

KU KARANTA: Kotu ta yanke hukuncin kwace kadarorin kamfanin P&ID

Manema labarai sun gano cewa mahaifiyar Musa ta gansa da igiya a yammacin jiya inda ta tambayesa amma sai ya ce zai je yin icce ne.

"A safiyar yau, an tsinci gawar Musa sagale a bishiya. A take aka kwance gawar tare da kai rahoto ofishin 'yan sanda," in ji wata majiya.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da tabbatar da cewa zasu bada bayani daga baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel