Tirkashi: 'Yan sanda zasu kama duk wani matashi da suka gani yana rike da wayar iPhone 11 daga nan zuwa Disamba

Tirkashi: 'Yan sanda zasu kama duk wani matashi da suka gani yana rike da wayar iPhone 11 daga nan zuwa Disamba

A yadda hukumar 'yan sandan kasar Ghana ta bayyana, sun gama shiryawa tsaf domin su kama duk wani matashi da suka gani yana rike da wayar iPhone 11 ko kuma iPhone 11 Pro Max

Sabuwar wayar iPhone 11 da iPhone 11 Pro Max wacce har yanzu ba a fitar da ita ba, ana sa ran za a fitar da ita a ranar 20 ga watan Satumbar nan, wayoyin da kudinsu ya kama daga dala dari takwas ($800) zuwa dala dubu daya da dari daya ($1100).

Wayar wacce har yanzu ba ta isa kasar Ghana ba hotunan ta sun riga sun gama zaga ko ina, tuni dai hukumar 'yan sandan kasar suka yi wani kwakkwaran gargadi musamman ga 'yan damfara ta yanar gizo da su lura sosai domin kuwa duk wanda suka gani da wannan wayar a hannu za su kama shi a take a wajen.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Usman Abubakar yayi luwadi da 'ya'yan uban gidanshi su 10 a jihar Sokoto

Wannan gargadi da hukumar 'yan sandan ta bayar tana nufin ta hana siyan wannan waya ko kuma amfani da ita, ko kuma duk wani dan sanda da yaga matashi yana amfani da wannan wayar ya cafke shi ya kaishi ofishin 'yan sanda domin bincike akan shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel