Babban magana: An gurfanar da wata uwargida kan daukar mijinta hoto ba tare da izininsa ba

Babban magana: An gurfanar da wata uwargida kan daukar mijinta hoto ba tare da izininsa ba

Rahotanni sun kawo cewa an gurfanar da wata mata yar shekara 33, Adeola Anofojie, wacce ake zargi da daukar hoton mijinta ba tare da izininsa ba, a gaban wata kotun Majistare da ke Ogudu, Lagas.

Anofojie na fuskantar tuhume-tuhume na haddasa rashin zaman lafiya da rashin bin ka’ida.

Dan sanda mai kara, Inspekta Donjour Perezi, ya bayyana cewa wacce ake karan ta aikata laifukan ne a ranar 23 ga watan Mayu a harabar kotun.

Perezi ya fada ma kotu cewa Adeola, wacce ta yi karar mijinta, Alexader Anojie, kan wani lamari na daban a ranar 23 ga watan Mayu, ta umurci Akinola Olusegu da ya dauki hotunan Anofojie a harabar kotu.

Dan sandan ya bayyana cewa laifukan sun saba ma sashi na 168 (1) (d) da 412 na dokar jihar Lagas na 2015.

Kamfanin dillancin labara Najeriya ta ruwaito cewa sashi na 168(2) ta sanya tarar N15,000 ga laifin farko sannan N40,000 ga sauran laifuffukan.

NAN ta kuma ruwaito cewa rashin bin ka’ida na nufin zaman gidan yari na watanni uku ga mai laifin.

Sai dai wacce ake kara, bata amsa tuhume-tuhumen da ake mata ba.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi rajiu’un: Uwa da yayanta 2 sun mutu bayan sun ci abinci, uban na cikin mawuyacin hali

Maishari’a, Ejiro Kubeinji ya bayar da belinta kan N100,000 tare da wadanda za su tsaya mata mutum biyu.

Kubeinje ya bayyana cewa lallai sai daya daga cikin wadanda za su tsaya mata ya kasance malami. Ya kuma dage sauraron karan zuwa ranar 2 ga watan Oktoba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel