Najeriya za ta kara ciyo bashin biliyan $2.5 daga bankin duniya

Najeriya za ta kara ciyo bashin biliyan $2.5 daga bankin duniya

Hafez Ghanem, mataimakin shugaban bankin duniya a nahiyar Afrika, ya ce suna magana da gwamnatin Najeriya a kan karbar rancen dalar Amurka biliyan $2.5.

Ghanem ya bayyana hakan ne yayin wata gana wa da shi ranar Laraba a Abuja, kamar yadda jaridar The Cable ta rawaito ranar Alhamis.

Mataimakin shugaban bankin ya ce Najeriya ta karbi rancen dalar Amurka biliyan $2.4 a shekarar 2018.

"Mu na magana da gwamnatin a kan karbar rance kusan adadin wadancan kudin da ta ranta domin daukan nauyin wasu aiyuka, adadin kudin zai kai $2.5bn," kamar yadda jaridar Bloomberg ta ce Ghanem ya fada.

"Ya na da matukar muhimmanci a wurin gwamnatin Najeriya ta gyara bangaren samar da wutar lantarki domin jan hankalin masu saka hannun jari. Dole gwamnatin ta samar da wutar lantarki domin ta rage kudin da 'yan kasuwa da masu saka hannu jari ke kashe wa wajen samar da wutar lantarki a kamfanoni da masana'antunsu.

"Najeriya kasa ce mai sa'a, saboda mafi yawan jama'arta matasa ne. Idan ana so a kirkiri aiyuka a Najeriya, ya zama wajibi a saka jari a harkokin inganta tattalin arziki na zamani," a cewarsa.

Ghanem ya ce bankin duniya zai bawa gwamnatin Najeriya goyon baya saboda kasar za ta iya farfado da tattalin arzikinta ta hanyar bunkasa kamfanoni da harkar noma.

DUBA WANNAN: Sojoji sun rufe ofishin wata kungiyar jin kai ta kasa da kasa a Maiduguri, sun kori ma'aikata

A cikin alkaluman da ofishin kula da harkokin bashin kudi (DMO) ya fitar, an samu karuwar biliyan N560 a matsayin kudin bashin da ake bin Najeriya daga watan Disamba na shekarar 2018 zuwa watan Maris na shekarar 2019.

Bashin da ake bin Najeriya a ketare ya kai tiriliyan N7.8 ($25.6bn), yayin da bashin cikin gida ya kai tiriliyan N17, kamar yadda alkaluma suka nuna a watan Maris na shekarar 2019.

Gwamnatin tarayya ta ce akwai gibin tiriliyan N1.86 a cikin kasafin kudin shekarar 2019 wanda take fatan za ta cike shi da kudaden da za ta ranto, amma majalisar dattijai ta rage gibin kudin zuwa tiriliyan N1.64 kafin ta zartar da kasafin kudin.

Da take jawabi a kan adadin kudaden da ake bin Najeriya bashi, ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce matsalar Najeriya ba ta kudaden da ake bi bashi bane, matsalar zurarewa da tattara kudaden haraji ne ke damun Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel