Sojoji sun kwato mutum 8 daga hannun masu garkuwa a Kaduna

Sojoji sun kwato mutum 8 daga hannun masu garkuwa a Kaduna

Wasu mutum takwas da aka sace a kan babbar hanyar Birnin Gwari dake jihar Kaduna a ranar Laraba, sun samu sun kubuta daga hannun miyagun.

Dakarun sojin 1 Division dake Kaduna a karkashin Operation Whirl Punch ne suka kwato su daga hannun ‘yan ta’addan.

KU KARANTA:Kai mutum ne mai amana, Keyamo ya yabawa Pantami

Majiyar kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ta sanar damu cewa, dakarun sun kama barayin ne bayan sun gano mabuyarsu a kauyen Labi dake a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Da misalin biyar na yammacin Laraba ne aka kubutar da mutanen jim kadan bayan masu garkuwan sunyi gaba da su.

Mutanen da aka sacen dai su na kan hanyar zuwa Kano ne daga Ilorin kamar yadda wata majiyar sojojin ta shaidawa NAN.

Majiyar ta bada tabbacin cewa an samu damar ceto mutanen ne bayan anyi amfani da bayanai na musamman game da mabuyar barayin.

Majiyar sojin ta ce: “An dauki tsawon lokaci muna barin wuta a daidai wuri da masu garkuwa suke a boye, hakan ne ya sanya suka arce suka bar wurin ba tare da shiri ba.”

Bugu da kari, wannan shi ne karo na biyu da dakarun sojin 1 Division ke kwato mutane daga hannun masu garkuwa cikin makonni biyu kacal.

Babban kwamandan 1 Division, Manjo Janar Faruk Yahaya ya jinjinawa dakarun sojin bisa wannan namijin kokarin da suka yin a ceto rayuwar bayin Allan da aka kama. Kana kuma da irin kokarin da suke cigaba da yi na ganin su kauda miyagun ayyuka.

https://www.dailytrust.com.ng/troops-rescue-8-kidnap-victims-in-kaduna.html

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel