Kotu ta yi watsi da bukatar APC, ta tabbatar wa da gwamnan PDP nasararsa

Kotu ta yi watsi da bukatar APC, ta tabbatar wa da gwamnan PDP nasararsa

Kotun sauraron korafin zaben gwamna da ke zamanta a Uyo, babban birnin jihar Uyo, ta tabbatar wa da gwamnan jihar, Udom Emmanuel, nasarar da ya samu ta lashe zaben kujerar gwamna da aka yi ranar 9 ga watan Maris, 2019.

A hukuncin da babban alkalin kotun, Jastis A.M. Yakubu, ya karanta bisa amincewar sauran alkalan kotun su biyu, kotun ta ce, "tun da babu wata sahihiyar shaida da masu kara zasu gabatar wa domin tabbatar da zargin da suke yi a kan isowar kayan zabe, kotun sauraron korafin zabe ta yi watsi da shaidar da suka gabatar."

Kotun ta ce shaidar takardu kadai, ba tare da sautin murya ba, ba zasu wadatar ba a irin zargin da masu kara ke yi ba, tare da bayar da misali da wani hukunci da kotun koli ta yanke a wata kara tsakanin Nweke da INEC.

A cewar hukuncin kotun, dukkan shaidun da masu kara suka gabatar domin kare ikirarinsu na cewa Obong Nsima Ekere ne ya lashe zaben kujerar gwamnan, ba su samu shiga ba a wurinta, a saboda haka ba ta gamsu da su ba.

DUBA WANNAN: Ina goyon bayan rufe iyakokin Najeriya dari bisa dari - Sarki Sanusi II

Jastis Yakubu ya kara da cewa masu kara sun gaza bin dokokin kotun wajen lissafa wa tare da gabatar da shaidunsu domin kare karar da suka shigar a gaban kotun.

Kotun ta bayyana cewa takardun shaidun da masu kara suka gabatar basu da alaka da korafin da suka shigar a gabanta tare da bayyana cewa mafi yawan takardun ba daga hannun hukuma suka fito, a same su ne a kwararo.

Masu kara, Obong Nsima Ekere; dan takarar gwamna a jihar Akwa Ibom, da jam'iyyar APC, sun garzaya kotun ne domin kalubalantar nasarar da Udom Emmanuel ya sake samu a zaben gwamna da aka yi ranar 9 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel