Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari na cikin ganawar sirri da shugabannin tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 19 ga watan Satumba ya yi ganawar sirri tare da shugabannin tsaro a fadar shugaban kasa, Abuja.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa ganawar na zuwa ne kusan sa’o’i 24 bayan anyi umurnin dakatar da shugabar ma’aikatan tarayya, Misis Winifred Oyo-Ita har sai illa-ma-shaa Allah.

Wani jawabi daga ofishin babban gwamnatin tarayya a ranar Laraba, 18 ga watan Satumba, ya bayyana cewa an dakatar da Oyo-Ita da ne domin ba hukumar yaki da cin hanci da rashawa damar kammala bincikenta.

Sai dai manema labarai basu san ajendar ganawar tasu ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Amma NAN ta tattaro cewa babu mamaki shugabannin tsaro za su sanar da Shugaban kasar game da ci gaban da aka samu ta bangaren tsaron kasa a yayinda Buhari ke shirin zuwa taron majalisar dinkin duniya.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi rajiu’un: Uwa da yayanta 2 sun mutu bayan sun ci abinci, uban na cikin mawuyacin hali

Shugaban kasar dai na shirin halartan taron majalisar UN na 74 a birnin New York a raar 22 ga watan Sarumba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel