Hari kan gidajen mai: Iran tayi martani kan sabbin takunkumin da Amurka ta saka mata

Hari kan gidajen mai: Iran tayi martani kan sabbin takunkumin da Amurka ta saka mata

Ministan harkokin kasashen waje na Iran ya yi Allah-wadai ta umurnin da saka sabbin tukunkumi kan kasar sakamakon hare-haren da aka kai a ma'ajiyar man fetur na kasar Saudiya a karshen makon da ya gabata da Saudiyya da Amurka su ke zargin Iran ta kai wa.

Shugaban Amurka, Shugaba Donald Trump ya umurci Sashi ajiya na kasar ta tsananta takunkumin da aka sanya wa Iran bayan hare-haren na bama-bamai da ya janyo gobara a matatun man fetur biyu na Saudiya na kamfanin Aramco da ya sanya farashin man su kayi tashin gauran zabi.

A halin yanzu dai ba a san takamamen takunkumin da Trump ya bayar da umurnin saka wa ba.

Da ya ke mayar da martani a shafin Twitter, Ministan harkokin kasashen waje na Iran Mohammad Javad Zarif ya kira matakin na Amurka a matsayin 'ta'addanci na tattalin arziki, saba doka da kuma rashin tausayi.'

DUBA WANNAN: An bayyana yadda 'yan bindiga suka bi wani basaraken arewa har gida suka kashe shi

Kasar Iran ta musanta cewa tana da hannu cikin harin da sakataren kasar Amurka Mike Pompeo a ranar Laraba ya kira harin a matsayin yunkurin yaki.

Amurka ta fara yiwa kasar Iran matsin lamba ne bayan ta janye daga yarjejeniyar nukiliya da kasashen biyu suka rattaba hannu a kai a shekarar 2015 inda ta fara neman sauran manyan kasashen duniya su saka wa Iran din takunkumi.

Hare-haren da aka kai da jirage marasa matuka da makamai masu linzami a cewar Saudiyya ya asasa rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran tare da sanya farashin man fetur yin tsada.

Kungiyar masu tayar da kayan baya na Houthi sun dauki nauyin kai hare-haren amma sakataren Amurka Pompeo ya yi ikirarin cewa karya su keyi kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel