Sojoji sun rufe ofishin wata kungiyar jin kai ta kasa da kasa a Maiduguri, sun kori ma'aikata

Sojoji sun rufe ofishin wata kungiyar jin kai ta kasa da kasa a Maiduguri, sun kori ma'aikata

Dakarun rundunar sojin Najeriya sun mamaye ofishin kungiyar jin kai ta kasa da kasa (Action Against Hunger) da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Wasu shaidu sun bayyana cewa sojojin sun rufe ofishin kungiyar ne a daren ranar Laraba, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Wakilin jaridar ya ga motocin sojoji guda biyu a bakin kofar shiga ofishin kungiyar da safiyar ranar Alhamis.

Wasu ma'aikatan kungiyar sun shaida wa Premium Times cewa dakarun soji sun kore su tare da yi musu gargadin su nesanta kansu da ofishin.

Ma'aikatan kungiyar sun ce sun tarar da sojoji dauke da bindigu, suna muzurai, yayin da suka isa ofishin da safiyar ranar Alhamis domin yin aiki kamar yadda suka saba kowacce rana.

"Ba mu san mene ne yake faruwa ba, sojoji sun hana mu shiga cikin ofishin kuma sun ki yin magana da kowa," kamar yadda wani ma'aikacin kungiyar da bai yarda a ambaci sunansa ba ya shaida wa jaridar Premium Times.

DUBA WANNAN: Jerin al'amura 5 da Buhari ya amince da su domin murnar cika shekaru 59 da samun 'yancin Najeriya

Kakakin rundunar soji ta 7, Ado Isa, bai amsa kiran wayar jaridar Premium Times ba, kazalika bai bayar da amsar sakon ko ta kwana da aka aika masa ba.

Kazalika, Premium Times ta ce Ayodele Famuyiwa, jami'in soji mai kula da harkokin sadarwa a rundunar atisaye ta 'Lafiya Dole' bai bayar amsar sakon da ta aika masa a kan lamarin.

Babban darektan kungiyar na Najeriya, Shashwat Saraf, ya tabbatar wa da jaridar faruwar lamarin a hirarsu ta wayar tarho.

Sai dai, ya bayyana cewa har yanzu rundunar soji ba ta tuntube su a kan dalilin rufe ofishinsu na Maiduguri ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel