Kuyi amfani da fasahar zamani domin kawo karshen matsalar tsaro – Gwamnatin tarayya ta shawarci gwamnoni

Kuyi amfani da fasahar zamani domin kawo karshen matsalar tsaro – Gwamnatin tarayya ta shawarci gwamnoni

Ministan tsaron cikin gidan Najeriya, Rauf Aregbesola ya yi kira ga Gwamnonin Najeriya musamman wadanda ke shugabancin jihohin Arewa maso Gabas da kuma maso Yamma da suyi koyi da gwamnatin Kaduna wurin kawo karshen matsalar tsaro.

Aregbesola ya ce amfani da hanyoyin zamani wurin kawo karshen matsalar tsaro kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ke yi abu mai matukar muhimmanci.

KU KARANTA:Balarabe na so a mika shugabancin kasa zuwa ga Kudu maso Gabas a 2023

Ministan yayi wannan furucin ne a yau Alhamis 19 ga watan Satumba yayin da yake karbar bakuncin Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i a ofishinsa dake Abuja.

A cewar ministan matsalar rashin tsaro aba ce wadda ta mamaye kusan ko ina a fadin duniyar nan. A don haka akwai bukatar amfani da cigaban zamani domin magance wannan matsala.

“Ta hanyar amfani da hanyoyin fasahar zamani zamu iya kawar da matsalar ‘yan bindiga, barayin shanu, garkuwa da mutane da kuma sauran matsalolin da suka shafi tsaro cikin dan kankanin lokaci a kasar nan.” Inji ministan.

Bugu da kari, ya sake cewa yin amfani da fasahar zamani wurin yaki da matsalolin tsaron zai kawo gagarumin cigaba, musamman a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.

Majiyar Channels Television ta kawo mana cewa, Aregbesola ya bayyana muhimmancin tsaro ga rayuwa, dukiya da kuma tattalin arzikin kasa wanda ta hanyar samun wadannan abubuwan ne kadai cigaba zai iya samuwa.

Da yake yabawa gwamnan bisa ziyarar da ya kawo masa, Aregbesola ya ce, magance matsalar tsaro na bukatar hadin hannu tsakanin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi saboda tsananin girman da al’amarin ya ke da shi.

https://www.channelstv.com/2019/09/18/fg-asks-governors-to-use-modern-technology-in-tackling-insecurity/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel