A ba mu kashi 40% na mukaman Gwamnati Inji Shugaban Matasan APC

A ba mu kashi 40% na mukaman Gwamnati Inji Shugaban Matasan APC

Bangaren Matasan APC mai mulki a Najeriya, sun yi kira ga gwamnati ta tabbatar ta ware kashi 40% na kujeru domin matasan kasar. Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ta rahoto wannan.

‘Ya ‘yan jam’iyyar ta APC sun yi wannan kira ne ta bakin shugabansu na kasa baki daya watau Sadiq Abubakar. Abubakar ya yi wannan kira ne a Ranar Larabar nan, 18 ga Watan Satumba.

Mista Sadiq Abubakar yake cewa su na son ganin an ba su kashi 40 na mukaman manyan kujerun ma’aikatu da hukumomin gwamnati. Hakan na zuwa ne bayan sun rasa wuri a FEC.

Matasan jam’iyyar sun yi wani taro ne a Garin Abuja inda Jagoran su ya ce: “Mu na sa ran kashi 40 na kujeru su tafi hannun Matasa, mu na sa ran a bamu shugabancin hukumomi da ma’aikatu.”

Sadiq Abubakar ya ke cewa da sauran ‘Yan uwan na sa Matasa a Birnin Tarayya cewa: “Babu wani Matashi ‘dan uwanmu a cikin sabuwar majalisar zartarwar tarayya ta Ministocin da aka kafa.”

KU KARANTA: Wani Babban Lauya a Najeriya ya soki Gwamnatin Buhari

Matashin ya nemi a duba kokarin da Matasan kasar su ka yi a lokacin zaben 2019, tare da kara cewa akwai bukatar a samu yadda za a cirewa Matasan Najeriya son fita kasashen waje su nemi aiki.

Bugu da kari, Abubakar ya ce sun tattauna yadda za su ga an ba Matasa damar juya akalar kasar nan tare da kawo manufofin da za su yi tasiri wajen taimakawa masu matsakaicin shekaru a kasar.

An ta kukan cewa wannan gwamnati ba ta damawa da matasa wajen gudanar da mulki. A cikin Ministoci 43 da aka nada kwanaki, babu wani Matashi ko mai kasa da shekara 40 ko mutum guda.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel