Balarabe na so a mika shugabancin kasa zuwa ga Kudu maso Gabas a 2023

Balarabe na so a mika shugabancin kasa zuwa ga Kudu maso Gabas a 2023

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Balarabe Musa, ya bayar da shawarar cewa a bari yankin kudu maso gabashin kasar ta samar da shugaban kasa na gaba a 2023.

Ya yi bayanin cewa akwai bukatar yin hakan domin tabbatar da daidaito, adalci da kuma gaskiya a tsakanin yan Najeriya da kuma ra'ayin kasar baki daya.

Balarabe ya amince da cewa mika shugabancin kasa na gaba zuwa yankin zai ba yan kabilar Igbo karfin gwiwar cewa suma yan Najeriya ne tare da inganta hadin kan kasar.

Ya bada shawaran cewa idan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala wa'adin mulkinsa a 2023, toh yankin Kudu maso Gabas ne ya kamata ta tsayar da shugaban kasa ba gaba, ba tare da la’akari da wace jami’a zata tsayar da dan takarar ba.

A cewar tsohon gwamnan, tunda yankunan Arewa, Kudu maso Yamma da kuma Kudu sun riki mukamin shugaban kasa, ba daidai bane idan yankunan suka yi takara da yankin Kudu maso Gabas a 2023 saboda bata dandana mulki ba tun da aka koma mulkin damokardiyya a 1999.

Har ila yau ya bayyana cewa zai zama son kai da rashin adalci idan dan Arewa ya tsaya takaran shugaban kasa bayan kammala mulkin Shugaban kasa Buhari na shekaru takwas.

Balarabe duk da haka yayi korafin cewa duk da kasancewar yankin Arewa a mulki na lokaci mai tsawo, yankin ta kasance koma baya ta fannin ci gaba a kasar.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya ta karyata ikirarin cewa Maiduguri na karkashin hari Read

Don haka ya bukaci jam’iyyun siyasa dasu duba yiwuwar zabar dan takaran shugaban kasa daga yankin Kudu maso Gabas a 2023.

Tsoho gwamnan yayi gargadin cewa fitar da yankin daga shugabancin kasar na iya haifar da hargitsin siyasa a kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel